30
“Amma yanzu suna yi mini ba’a
waɗanda na girme su,
waɗanda iyayensu maza ba su isa
su zama karnukan kiwon garken tumakina ba.
Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni,
tun da ba su da sauran kuzari?
Duk sun rame don rashi da yunwa,
suna yawo a gaigayar ƙasa
a kufai da dare.
A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi,
jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu.
An kore su daga cikin mutanensu,
aka yi musu ihu kamar ɓarayi.
An sa dole su zauna a kwazazzabai da kuma
cikin kogunan duwatsu da kuma cikin ramummuka cikin ƙasa.
Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji,
suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya.
Mutane marasa hankali marasa suna,
an kore su daga ƙasar.
 
“Yanzu kuma ’ya’yansu maza su suke yi mini ba’a cikin waƙa
na zama abin banza a gare su.
10 Suna ƙyamata suna guduna;
suna tofa mini miyau a fuska.
11 Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala
sun raba ni da mutuncina.
12 A hannun damana ’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar;
sun sa tarko a ƙafafuna,
sun yi shirin hallaka ni.
13 Sun ɓata mini hanyata;
sun yi nasara cikin hallaka ni,
ba tare da wani ya taimake su ba.
14 Suka nufo ni daga kowane gefe;
suka auko mini da dukan ƙarfinsu.
15 Tsoro ya rufe ni;
an kawar mini mutuncina kamar da iska,
dukiyata ta watse kamar girgije.
 
16 “Yanzu raina yana ƙarewa;
kwanakin wahala sun kama ni.
17 Dare ya huda ƙasusuwana;
ina ta shan azaba ba hutawa.
18 A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina;
ya shaƙe ni kamar wuyan rigata.
19 Ya jefa ni cikin laka,
na zama ba kome ba sai ƙura da toka.
 
20 “Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba.
Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai.
21 Ka dube ni ba tausayi;
Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka.
22 Ka ɗaga ni sama ka ɗora ni a kan iska;
ka jujjuya ni cikin hadari.
23 Na san za ka sauko da ni ga mutuwa
zuwa wurin da kowane mai rai zai je.
 
24 “Ba shakka ba mai ɗora hannu a kan mutumin da yake cikin wahala.
Lokacin da ya yi kukan neman taimako a cikin wahalarsa.
25 Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba?
Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba?
26 Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau,
mugun abu ne ya zo;
Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo.
27 Zuciyata ba tă daina ƙuna ba;
ina fuskantar kwanakin wahala.
28 Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba.
Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako.
29 Na zama ɗan’uwan diloli,
na zama abokan mujiyoyi.
30 Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa;
jikina yana ƙuna da zazzaɓi.
31 Garayata ta zama ta makoki,
sarewata kuma ta zama ta kuka.