31
“Na yi alkawari da idanuna
kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.
Gama mene ne rabon mutum daga Allah a sama,
gādonsa daga Maɗaukaki a sama?
Ba masifa ba ne domin mugaye,
hallaka kuma ga waɗanda suka yi ba daidai ba?
Bai ga hanyoyina ba ne
bai ƙirga kowace takawata ba?
 
“In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya
ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya,
Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya
zai kuma san cewa ni marar laifi ne.
In takawata ta kauce daga hanya,
in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so,
ko kuma in hannuwana suna da laifi;
bari waɗansu su ci abin da na shuka,
kuma bari a tuge amfanin gonata.
 
“In sha’awar mace ya shiga mini zuciya,
ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
10 sai matata ta niƙa hatsin wani
kuma waɗansu maza su kwana da ita.
11 Gama wannan zai zama abin kunya,
zunubin da za a yi shari’a a kai.
12 Wuta ce take ƙuna har ta hallakar;
za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.
 
13 “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu,
sa’ad da suke da damuwa da ni,
14 me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni?
Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?
15 Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba?
Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?
 
16 “In na hana wa matalauta abin da suke so,
ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,
17 in na ajiye burodina don kaina kaɗai,
ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,
18 amma tun suna tasowa na lura da su,
kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.
19 In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura,
ko wani mai bukata da ba shi da riga,
20 kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba
don na yi masa sutura da gashin tumakina,
21 in na ɗaga hannuna don in cuci maraya,
domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,
22 bari hannuna yă guntule daga kafaɗata,
bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.
23 Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah,
kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.
 
24 “In na dogara ga zinariya
ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’
25 in na yi fahariya don yawan dukiyata,
arzikin da hannuwana suka samu.
26 In na dubi rana cikin haskenta,
ko kuma wata yana tafiyarsa,
27 zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye,
hannuna kuma ya sumbace su.
28 Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan
don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.
 
29 “In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina;
ko kuma domin wahala ta same shi,
30 ban bar bakina yă yi zunubi
ta wurin la’anta shi ba,
31 in mutanen gidana ba su taɓa cewa,
‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’
32 Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi,
gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya,
33 in na ɓoye zunubina yadda mutane* suke yi,
ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,
34 domin ina tsoron taron mutane
kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini,
sai na yi shiru kuma ban fita waje ba.
 
35 (“Kash, da ina da wanda zai ji ni!
Na sa hannu ga abin da na faɗa don kāre kaina,
bari Maɗaukaki yă amsa mini; bari mai tuhumata da laifi yă yi ƙarata a rubuce.
36 Ba shakka sai in ɗora a kafaɗata,
zan aza a kaina kamar rawani.
37 Zan ba shi lissafin duk abin da na taɓa yi;
zan zo gabansa kamar ɗan sarki.)
 
38 “In ƙasata tana kuka da ni
kunyoyinta duk sun cika da hawaye,
39 in na kwashe amfaninta ban biya ba
ko kuma na kashe masu ita,
40 bari ƙaya ta fito a maimakon alkama
ciyawa kuma a maimakon sha’ir.”
Maganar Ayuba ta ƙare.
 
* 31:33 Ko kuwa yadda Adamu ya yi