7
Gargaɗi A kan mazinaciya
Ɗana, ka kiyaye kalmomina
ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.
Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu;
ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.
Ka daure su a yatsotsinka;
ka rubuta su a allon zuciyarka.
Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,”
ka kuma kira fahimi danginka;
za su kiyaye ka daga mazinaciya,
daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.
 
A tagar gidana
na leƙa ta labule mai rammuka.
Sai na gani a cikin marasa azanci,
na lura a cikin samari,
wani matashi wanda ba shi da hankali.
Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta,
yana tafiya a gefen wajen gidanta
da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa,
yayinda duhun dare yana farawa.
 
10 Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi,
saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi.
11 (Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya,
ƙafafunta ba sa zama a gida;
12 wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali,
tana yawo a kowace kusurwa.)
13 Sai ta kama shi ta rungume shi
da duban soyayya a fuskarta ta ce,
 
14 “Ina da hadaya ta salama a gida;
yau zan cika alkawarina.
15 Saboda haka na fito don in sadu da kai;
na neme ka na kuma same ka!
16 Na lulluɓe gadona
da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.
17 Na yayyafa turare a gadona
da mur, aloyes da kuma kirfa.
18 Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe;
bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!
19 Mijina ba ya gida;
ya yi tafiya mai nisa.
20 Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi
ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”
 
21 Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce;
ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.
22 Nan take, ya bi ta
kamar saniyar da za a kai mayanka,
kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo
23 sai da kibiya ta soki hantarsa,
kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko,
ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.
 
24 Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;
ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.
25 Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta
ko ku kauce zuwa hanyoyinta.
26 Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci;
kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.
27 Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari
mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.