8
Kiran hikima
Hikima ba ta yin kira ne?
Fahimi ba ya tā da muryarsa ne?
A ƙwanƙoli a kan hanya,
inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta;
kusa da ƙofofin shiga cikin birni,
a mashigai, ta tā da murya,
“Gare ku, ya mutane, nake kira;
na tā da muryata ga dukan ’yan adam.
Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali;
ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.
Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa;
na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai.
Bakina yana magana abin da yake gaskiya,
gama leɓunana sun ƙi mugunta.
Dukan kalmomin bakina suna da adalci;
babu waninsu da ya karkace ko kuwa ƙarya ne.
Ga mai tunani dukansu daidai ne;
ba su da laifi ga waɗanda suke da sani.
10 Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa,
sani a maimakon zinariya zalla,
11 gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja,
kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita.
 
12 “Ni, hikima, ina zama tare da hankali;
ina da sani da iya rarrabewa.
13 Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;
ina ƙin girman kai da fariya,
halin mugunta da kuma muguwar magana.
14 Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne;
ina da fahimi da kuma iko.
15 Ta wurina sarakuna suke mulki
masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;
16 ta wurina sarakuna suke mulki,
da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.
17 Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,
kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.
18 Tare da ni akwai wadata da girmamawa,
dukiya da wadata masu dawwama.
19 ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla;
amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.
20 Ina tafiya a hanyar adalci,
a kan hanyoyin gaskiya,
21 ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata
ina sa wuraren ajiyarsu su cika.
 
22 Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa,
kafin ayyukansa na tuntuni;
23 an naɗa ni tun fil azal,
daga farko, kafin duniya ta kasance.
24 Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni,
sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa;
25 kafin a kafa duwatsu a wurarensu,
kafin tuddai ma, an haife ni,
26 kafin ya yi duniya ko gonaki
ko wata ƙurar duniya.
27 Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu,
sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,
28 sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa
ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram,
29 sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa
domin kada ruwaye su zarce umarninsa,
da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.
30 A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa.
Na cika da murna kowace rana,
kullum ina farin ciki a gabansa,
31 ina farin ciki da dukan duniyarsa
ina murna da ’yan adam.
 
32 “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;
masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.
33 Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima;
kada ku ƙyale ta.
34 Mai albarka ne wanda ya saurare ni;
yana tsaro kullum a ƙofofina,
yana jira a ƙofar shigata.
35 Gama duk wanda ya same ni ya sami rai
zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
36 Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa;
dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.”