*
Zabura 112
Yabi Ubangiji.
 
Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,
wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.
 
’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar;
tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.
Wadata da arziki suna a cikin gidansa,
adalcinsa zai dawwama har abada.
Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya,
mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.
Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,
shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.
 
Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba;
za a tuna da mai adalci har abada.
Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba;
zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.
Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba;
a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.
Ya rarraba kyautansa ga matalauta,
adalcinsa zai dawwama har abada;
za a ɗaga ƙahonsa§ sama da bangirma.
 
10 Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi,
zai ciza haƙora yă kuma lalace;
sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.
* Zabura 112: Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi. Zabura 112:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya Zabura 112:4 Ko kuwa / gama Ubangiji mai alheri ne, mai tausayi da kuma mai adalci. § Zabura 112:9 Ƙaho a nan yana nufin girma.