Zabura 113
Yabi Ubangiji.*
 
Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji,
ku yabi sunan Ubangiji.
Bari a yabi sunan Ubangiji,
yanzu da har abada kuma.
Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa,
a yabi sunan Ubangiji.
 
Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai,
ɗaukakarsa a bisa sammai
Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu,
Wannan mai zama a kursiyi can bisa,
wanda yake sunkuya yă dubi
sammai da duniya?
 
Yakan tā da matalauta daga ƙura
yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;
ya zaunar da su tare da sarakuna,
tare da sarakunan mutanensu.
Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta
ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki.
 
Yabi Ubangiji.
* Zabura 113:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya, haka ma a aya 9.