Zabura 117
Yabi Ubangiji, dukanku al’umma;
ku ɗaukaka shi, dukanku mutane.
Gama ƙaunarsa da girma take gare mu,
amincin Ubangiji kuma madawwami ne har abada.
 
Yabi Ubangiji.*
* Zabura 117:2 Da Ibraniyanci Hallelu Ya