Zabura 118
Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
 
Bari Isra’ila yă ce,
“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
Bari gidan Haruna yă ce,
“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce,
“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
 
Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji,
ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.
Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai yi mini?
Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.
Zan yi nasara a kan abokan gābana.
 
Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga mutum.
Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga sarakuna.
10 Dukan al’ummai sun kewaye ni,
amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
11 Sun kewaye ni a kowane gefe,
amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
12 Sun rufe ni kamar ƙudan zuma,
amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta;
a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
13 An ture ni baya na kusa fāɗuwa,
amma Ubangiji ya taimake ni.
14  Ubangiji ne ƙarfina da waƙata;
ya zama mai cetona.
 
15 Sowa ta farin ciki da nasara
sun fito a cikin tentunan adalai,
“Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!
16 An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama;
hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!”
17 Ba zan mutu ba amma zan rayu,
zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi.
18  Ubangiji ya hore ni sosai,
amma bai ba da ni ga mutuwa ba.
19 Buɗe mini ƙofofin adalci;
zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji.
20 Wannan ne ƙofar Ubangiji
inda adalai za su shiga.
21 Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini;
ka zama mai cetona.
 
22 Zabura Dutsen da magina suka ƙi
ya zama mai amfani;
23  Ubangiji ne ya yi haka,
kuma abu mai daraja ne a idanunmu.
24 Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;
bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
 
25 Ya Ubangiji, ka cece mu;
Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.
 
26 Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji.
Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.
27  Ubangiji shi ne Allah
ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu.
Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki
ku kai su ƙahoni na bagade.
 
28 Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya;
kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.
 
29 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.