Zabura 127
Waƙar haurawa. Ta Solomon.
In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,
masu gininta suna wahala a banza ne.
In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,
masu tsaro suna yin tsaro a banza.
Banza ne ka farka da wuri
ka koma da latti,
kana fama don abincin da za ka ci,
gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
 
’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,
yara lada ne daga gare shi.
Kamar kibiyoyi a hannun jarumi
haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.
Mai albarka ne mutumin
da korinsa sun cika da su.
Ba za a kunyata su ba
sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.