Zabura 128
Waƙar haurawa.
Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,
waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
Za ka ci amfanin aikinka;
albarku da wadata za su zama naka.
Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya
a cikin gidanka;
’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun
kewaye da teburinka.
Ta haka mai albarka yake
wanda yake tsoron Ubangiji.
 
Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona
dukan kwanakin ranka;
bari ka ga wadatar Urushalima,
bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka.
Salama tă kasance tare da Isra’ila.