Zabura 13
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
Har yaushe, ya Ubangiji? Za ka manta da ni har abada ne?
Har yaushe za ka ɓoye fuskarka daga gare ni?
Har yaushe zan yi kokawa da tunanina
kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata?
Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina?
 
Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.
Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa;
abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,”
kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi.
 
Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa;
zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.
Zan rera ga Ubangiji
gama ya yi mini alheri.