Zabura 14
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda.
Wawaye sukan ce a ransu,
“Ba Allah.”
Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne;
babu wani da yake yi abu mai kyau.
 
Ubangiji ya duba daga sama
a kan ’yan adam
don yă ga ko akwai wani da ya gane,
wani wanda yake neman Allah.
Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu;
babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau,
ba ko ɗaya.
 
Masu aikata mugunta za su taɓa koyo.
 
Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa
kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?
Ga su, tsoro ya sha kansu,
gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai.
Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza,
amma Ubangiji ne mafakansu.
 
Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana!
Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa,
bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!