Zabura 132
Waƙar haurawa.
Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda
da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.
 
Ya yi rantsuwa ga Ubangiji
ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,
“Ba zan shiga gidana
ko in kwanta a gado ba,
ba zan ba wa idanuna barci ba,
ba gyangyaɗi wa idanuna,
sai na sami wuri wa Ubangiji,
mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”
 
Mun ji haka a Efrata,
muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar,*,
“Bari mu tafi wurin zamansa;
bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa,
ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka,
kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.
Bari a suturta firistocinka da adalci;
bari tsarkakanka su rera don farin ciki.”
 
10 Saboda Dawuda bawanka,
kada ka ƙi shafaffenka.
 
11  Ubangiji ya rantse wa Dawuda
tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa,
“Ɗaya daga cikin zuriyarka
zan sa a kan kursiyinka,
12 in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari
da farillan da na koya musu,
to ’ya’yansu maza za su zauna
a kan kursiyinka har abada abadin.”
 
13 Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona,
ya so ta zama mazauninsa,
14 “Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin;
a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,
15 zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa;
matalautanta za su ƙoshi da abinci.
16 Zan suturta firistocinta da ceto,
tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.
 
17 “A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda
in kuma kafa fitila saboda shafaffena.
18 Zan suturta abokan gābansa da kunya,
amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”
* Zabura 132:6 Wato, Kiriyat Yeyarim Zabura 132:6 Ko kuwa mun ji game da shi a Efrata, mun same shi a filayen Ya’ar. (Kuma babu alamar keɓewa kewaye da ayoyi 7-9) Zabura 132:17 Ƙaho a nan yana nufin wani mai ƙarfi, wato, sarki.