Zabura 133
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma
sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!
 
Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai,
yana gangarawa a gemu,
yana gangarawa a gemun Haruna,
har zuwa wuyan rigunansa.
Yana kamar raɓar Hermon
da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona.
Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa,
har ma rai na har abada.