Zabura 136
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Ku yi godiya ga Allahn alloli.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
 
Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Wanda ya yi manyan haskoki,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Rana don tă yi mulkin yini,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare;
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
 
10 Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
11 Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
12 Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko;
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
 
13 Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
14 Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
15 Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku;
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
 
16 Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
 
17 Wanda ya buge manyan sarakuna,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
18 Ya karkashe manyan sarakuna,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
19 Sihon sarkin Amoriyawa
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
20 Da kuma Og sarkin Bashan,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
21 Ya kuma ba da ƙasarsu gādo,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
22 Gādo ga bawansa Isra’ila;
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
 
23 Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
24 Ya kuma ’yantar da mu daga abokan gābanmu,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
25 Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
 
26 Ku yi godiya ga Allah na sama.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.