Zabura 135
Yabi Ubangiji.*
 
Yabi sunan Ubangiji;
yabe shi, ku bayin Ubangiji,
ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji,
cikin filayen gidan Allahnmu.
 
Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne;
rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau.
Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa,
Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.
 
Na san cewa Ubangiji yana da girma,
cewa shugabanmu ya fi dukan alloli girma.
Ubangiji yana yin abin da ya ga dama,
a sammai da kuma a duniya,
cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.
Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya;
yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama
ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.
 
Ya kashe ’ya’yan fari na Masar,
’ya’yan fari na mutane da na dabbobi.
Ya aiko da alamu da abubuwan banmamaki a tsirkiyarku, ya Masar,
a kan Fir’auna da kuma dukan bayinsa.
10 Ya bugi al’ummai masu yawa
ya kuma karkashe manyan sarakuna,
11 Sihon sarkin Amoriyawa,
Og sarkin Bashan
da kuma dukan sarakunan Kan’ana,
12 ya kuma ba da ƙasarsa kamar abin gādo,
abin gādo ga mutanensa Isra’ila.
 
13 Sunanka, ya Ubangiji, dawwammame ne har abada,
sanin da aka yi maka, ya Ubangiji, yana nan cikin dukan zamanai.
14 Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi
ya kuma ji tausayin bayinsa.
 
15 Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya,
da hannuwan mutane suka yi.
16 Suna da bakuna, amma ba sa magana,
idanu, amma ba sa gani;
17 suna da kunnuwa, amma ba sa ji,
ba kuwa numfashi a bakunansu.
18 Waɗanda suka yi su za su zama kamar su,
haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su.
 
19 Ya gidan Isra’ila, yabi Ubangiji;
Ya gidan Haruna, yabi Ubangiji;
20 Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji;
ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji.
21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona,
gare shi wanda yake zama a Urushalima.
 
Yabi Ubangiji.
* Zabura 135:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a ayoyi 3 da 21.