Zabura 141
Zabura ta Dawuda.
Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri.
Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.
Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa;
bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.
 
Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji;
ka yi tsaron ƙofar leɓunana.
Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu,
ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka
tare da mutane masu aikata mugunta;
kada ka bari in ci abincinsu.
 
Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne;
bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina.
Kaina ba zai ƙi shi ba,
duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.
 
Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse,
mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne.
Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa,
haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.”
 
Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka;
a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.
Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini,
daga tarkon da mugaye suka sa.
10 Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu,
amma bari ni in zo in wuce lafiya.