Zabura 142
Maskil ne* ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce.
Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji;
na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.
Na kawo gunagunina a gabansa;
a gabansa na faɗa wahalata.
 
Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina,
kai ne wanda ya san hanyata.
A hanyar da nake tafiya
mutane sun kafa mini tarko.
Duba ta damata ka gani;
babu wanda ya kula da ni.
Ba ni da mafaka;
babu wanda ya kula da raina.
 
Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
Na ce, “Kai ne mafakata,
rabona a ƙasar masu rai.”
 
Ka saurari kukata,
gama ina cikin matsananciyar bukata;
ka cece ni daga waɗanda suke fafarata,
gama sun fi ni ƙarfi sosai.
Ka ’yantar da ni daga kurkuku,
don in yabi sunanka.
Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni
saboda alherinka gare ni.
* Zabura 142: Kan maganar, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.