Zabura 143
Zabura ta Dawuda.
Ya Ubangiji, ka ji addu’ata,
ka saurari kukata don neman jinƙai;
cikin amincinka da adalcinka
ka amsa mini.
Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a,
gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.
Abokin gāba yana fafarata,
ya murƙushe ni har ƙasa;
ya sa ina zama a cikin duhu
kamar waɗanda suka mutu tun tuni.
Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina
zuciyata ta damu ƙwarai.
Na tuna da kwanakin baya
na yi tunani a kan dukan ayyukanka
na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.
Na buɗe hannuwana gare ka;
raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa.
Sela
 
Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji;
ƙarfina ya ƙare.
Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni
in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.
Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,
gama na sa zuciyata a gare ka.
Ka nuna mini hanyar da zan bi,
gama a gare ka na miƙa raina.
Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji,
gama na ɓoye kaina a gare ka.
10 Ka koya mini in yi nufinka,
gama kai ne Allahna;
bari nagarin Ruhunka
yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.
 
11 Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina;
a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.
12 A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana;
ka hallaka dukan maƙiyana,
gama ni bawanka ne.