Zabura 2
Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki
mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?
Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi
masu mulki sun taru gaba ɗaya
suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.
Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu,
mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”
 
Mai zama a kursiyi a sama yana dariya;
Ubangiji yana musu ba’a.
Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa
ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,
“Na kafa Sarkina a kan kursiyi
a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”
Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji.
Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne;
yau na zama Mahaifinka.
Ka tambaye ni
zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka,
iyakokin duniya su zama mallakarka.
Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe;
za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”
 
10 Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo;
ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya.
11 Ku bauta wa Ubangiji da tsoro
ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.
12 Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi
ku hallaka a abubuwan da kuke yi,
gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya.
Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.