Zabura 23
Zabura ta Dawuda.
Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,
Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,
yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,
yakan maido da raina.
Yakan bi da ni a hanyoyin adalci
saboda sunansa.
Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,*
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
 
Ka shirya mini tebur
a gaban abokan gābana.
Ka shafe kaina da mai;
kwaf nawa ya cika har yana zuba.
Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
* Zabura 23:4 Ko kuwa ta kwarin mafi duhu duka