Zabura 24
Zabura ta Dawuda.
Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta,
duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;
gama ya gina ta a kan tekuna
ya kafa ta a kan ruwaye.
 
Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?
Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?
Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,
wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki
ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.
 
Zai sami albarka daga Ubangiji
da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan,
waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub.
Sela
 
Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi;
ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi,
don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka?
Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko,
Ubangiji mai girma a yaƙi.
Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi;
ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi,
don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
10 Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka?
Ubangiji Maɗaukaki,
shi ne Sarkin ɗaukaka.
Sela