Zabura 26
Ta Dawuda.
Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji,
gama na yi rayuwa marar zargi;
Na dogara ga Ubangiji
ba tare da kaucewa ba.
Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni,
ka bincike zuciyata da tunanina;
gama ƙaunarka kullum tana a gabana,
kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.
 
Ba na zama tare da masu ruɗu,
ko in yi tarayya da masu riya;
na ƙi jinin taron masu aikata mugunta
na ƙi in zauna tare da mugaye.
Na wanke hannuwana cikin rashin laifi,
ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,
ina shelar yabonka da ƙarfi
ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.
 
Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji,
wurin da ɗaukakarka ke zaune.
Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi
raina tare da masu son yin kisankai
10 waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu,
waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
11 Amma na yi rayuwa marar zargi;
ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.
 
12 Ƙafafuna suna tsaye daram;
cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.