Zabura 28
Ta Dawuda.
A gare ka nake kira,
ya Ubangiji Dutsena;
kada ka yi mini kunnen ƙashi.
Gama in ka yi shiru,
zan zama kamar waɗanda suka gangara rami.
Ka ji kukata ta neman jinƙai
yayinda nake kira ka don neman taimako,
yayinda nake daga hannuwana
wajen Wurinka Mafi Tsarki.
 
Kada ka ja ni tare da mugaye,
tare da masu yin mugunta,
masu magana kamar ta alheri ce da maƙwabtansu
amma suna riƙe da su a zukatansu.
Ka sāka musu da ayyukansu
da kuma don mugun aikinsu;
ka sāka musu saboda abin da hannuwansu suka yi
ka kuma mayar musu abin da ya dace da su.
 
Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji
da abin da hannuwansa suka yi ba,
zai rushe su
ba kuwa zai ƙara gina su ba.
 
Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya ji kukata na neman jinƙai.
Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
 
Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa,
kagarar ceto domin shafaffensa.
Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka;
ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada.