*
Zabura 43
Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah,
ka kuma nemi hakkina
a kan al’ummai marasa sanin Allah.
Ka kuɓutar da ni daga
masu ruɗu da mugayen mutane.
Kai ne Allah mafakata.
Me ya sa ka ƙi ni?
Me zai sa in yi ta yawo ina makoki,
a danne a hannun abokin gāba?
Ka aiko da haskenka da gaskiyarka,
bari su bishe ni
bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki,
zuwa wurin da kake zama.
Sa’an nan zan tafi bagaden Allah,
ga Allah, farin cikina da murnata.
Zan yabe ka da garaya,
Ya Allah, Allahna.
 
Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?
Me ya sa ka damu a cikina?
Ka dogara ga Allah,
gama zai sāke yabe shi,
Mai Cetona da Allahna.
* Zabura 43: Cikin rubuce-rubucen hannu masu yawa a Ibraniyanci Zabura 42 da 43 zabura guda ce.