Zabura 44
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’ya’yan Kora maza. Maskil* ne.
Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah;
kakanninmu sun faɗa mana
abin da ka aikata a kwanakinsu,
tun dā can.
Da hannunka ka kori al’ummai
ka kuma dasa kakanninmu;
ka ragargaza mutanen
ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka.
Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar,
ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba;
hannun damanka ne, ƙarfin hannunka,
da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.
 
Kai ne Sarkina da kuma Allahna,
wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.
Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya;
ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu.
Ba na dogara ga bakana,
takobina ba ya kawo nasara;
amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu,
ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.
A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini,
kuma za mu yabi sunanka har abada.
Sela
 
Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu;
ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.
10 Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba,
kuma abokan gābanmu suka washe mu.
11 Ka ba da mu a cinye kamar tumaki
ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.
12 Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba
babu wata riba daga sayar da su da ka yi.
 
13 Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu,
abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
14 Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai;
mutanen suna kaɗa mana kai.
15 Dukan yini ina cikin wulaƙanci,
fuskata kuma ta rufu da kunya
16 saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina,
saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.
 
17 Dukan wannan ya faru da mu,
ko da yake ba mu manta da kai ba
ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.
18 Zukatanmu ba su juya baya;
ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.
19 Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji
ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.
 
20 Da a ce mun manta da sunan Allahnmu
ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,
21 da Allah bai gane ba,
da yake ya san asiran zuciya?
22 Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini;
aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.
 
23 Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci?
Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.
24 Me ya sa ka ɓoye fuskarka
ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?
 
25 An kai mu ƙasa zuwa ƙura;
jikunanmu sun manne da ƙasa.
26 Ka tashi ka taimake mu;
ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.
* Zabura 44: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.