Zabura 46
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.
Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza
duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
ko da ruwansa suna ruri suna kumfa
duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu.
Sela
 
Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna,
tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.
Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba;
Allah zai taimake ta da safe.
Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi;
ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.
 
Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;
Allah na Yaƙub ne kagararmu.
Sela
 
Zo ku ga ayyukan Ubangiji,
kangon da ya kawo a kan duniya.
Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit
ko’ina a duniya.
Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu,
ya ƙone garkuwoyi* da wuta.
10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;
za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,
za a ɗaukaka ni cikin duniya.”
 
11  Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;
Allah na Yaƙub ne kagararmu.
Sela
* Zabura 46:9 Ko kuwa kekunan yaƙi