Zabura 45
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Lili.” Na ’ya’yan Kora maza. Maskil* Waƙar Aure.
Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana
yayinda nake rera ayoyina wa sarki;
harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci.
 
Kai ne mafi kyau cikin mutane
an kuma shafe leɓunanka da alheri,
da yake Allah ya albarkace ka har abada.
 
Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi;
ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja.
Cikin darajarka ka hau zuwa nasara
a madadin gaskiya, tawali’u da adalci;
bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki.
Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki;
bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka.
Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin;
sandar adalci zai zama sandar mulkinka.
Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta;
saboda haka Allah, Allahnka, ya sa ka a bisa abokanka
ta wurin shafe ka da man farin ciki.
Dukan rigunanka suna ƙanshin turaren mur da na aloyes, da na kashiya;
daga kowace fadan da aka yi masa ado da hauren giwa
kaɗe-kaɗen tsirkiya kan sa ka murna.
’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama;
a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya.
 
10 Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne,
Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki.
11 Sarki ya cika da sha’awar kyanki;
ki girmama shi, gama shi ne maigidanki.
12 Diyar Taya za tă zo da kyauta,
mawadata za su nemi tagomashinki.
13 Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun;
an saƙa rigarta da zaren zinariya.
14 Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki;
abokanta budurwai suna biye da ita
aka kuwa kawo su gare ka.
15 Aka bi da su cikin farin ciki da murna;
suka shiga fadan sarki.
 
16 ’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka;
za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar.
 
17 Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai;
saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin.
* Zabura 45: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.