Zabura 54
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil* ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?”
Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka;
ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.
Ka ji addu’ata, ya Allah;
ka saurari maganar bakina.
 
Baƙi suna kawo mini hari;
mutane marasa imani suna neman raina,
mutanen da ba sa tsoron Allah.
Sela
 
Tabbatacce Allah ne mai taimakona,
Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.
 
Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina;
cikin amincinka ka hallaka su.
 
Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka;
zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.
Gama ya cece ni daga dukan wahalolina,
idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.
* Zabura 54: Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.