Zabura 55
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil* ta Dawuda.
Ka ji addu’ata, ya Allah,
kada ka ƙyale roƙona;
ka ji ni ka kuma amsa mini.
Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis
hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina,
saboda danniyar mugaye.
Gama sukan jawo mini wahala,
suna jin haushina suna ƙina.
 
Zuciyata tana wahala a cikina;
tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina.
Tsoro da rawan jiki sun kama ni;
razana ta sha kaina.
Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana!
Ai, da na yi firiya na tafi na huta,
da na tafi can da nisa
na zauna a hamada;
Sela
da na hanzarta na tafi wurin mafakata,
nesa da muguwar iska da hadiri.”
 
Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,
gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.
10 Dare da rana suna yawo a kan katanga;
mugun hali da zargi suna a cikinta.
11 Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni;
barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta.
 
12 Da a ce abokin gāba ne ke zagina,
da na jure da shi;
da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina,
da na ɓoye daga gare shi.
13 Amma kai ne, mutum kamar ni,
abokina, abokina na kurkusa,
14 wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai
yayinda muke tafiya tare
a taron jama’a a gidan Allah.
 
15 Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari;
bari su gangara da rai zuwa cikin kabari,
gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu.
 
16 Amma na kira ga Allah,
Ubangiji kuwa ya cece ni.
17 Safe, rana da yamma
ina kuka da nishi,
yakan kuwa ji muryata.
18 Yakan fisshe ni lafiya
daga yaƙin da ake yi da ni,
ko da yake da yawa suna gāba da ni.
19 Allah, yana mulki har abada,
zai ji su yă kuma azabtar da su,
Sela
mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu
kuma ba sa tsoron Allah.
 
20 Abokina ya kai wa abokansa hari;
ya tā da alkawarinsa.
21 Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun,
duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa;
kalmominsa sun fi mai sulɓi,
duk da haka takuba ne zārarru.
 
22 Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
23 Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye
zuwa cikin ramin lalacewa;
masu kisa da mutane masu ruɗu
ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba.
 
Amma ni dai, na dogara gare ka.
* Zabura 55: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.