Zabura 57
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.* Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo.
Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai,
gama a gare ka raina yake samun mafaka.
Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka
sai masifar ta wuce.
 
Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka,
ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.
Ya aika daga sama ya kuwa cece ni,
yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi;
Sela
Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.
 
Ina tsakiyar zakoki;
ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane,
mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi,
waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.
 
Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
 
Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna,
damuwa ta sha ƙarfina.
Sun haƙa rami a hanyata,
amma su kansu suka fāɗa a cikinta.
Sela
 
Zuciyata tana nan daram, ya Allah,
zuciyata tana nan daram;
zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
Ka farka, raina!
Ku farka, garaya da molo!
Zan sa safe yă farka.
 
Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai a cikin mutane.
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;
amincinka na kaiwa sarari.
 
11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
* Zabura 57: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.