Zabura 58
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.*
Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai?
Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?
Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci,
da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya.
 
Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce;
daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata.
Dafinsu ya yi kamar dafin maciji,
kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa,
da ba ya jin muryar gardi,
kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama.
 
Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah;
ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji!
Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa;
sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke.
Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya,
kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana.
 
Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa,
ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.
10 Masu adalci za su yi murna sa’ad da aka rama musu,
sa’ad da suka wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.
11 Sa’an nan mutane za su ce,
“Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai;
tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.”
* Zabura 58: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Zabura 58:9 Ma’anar Ibraniyancin wannan aya ba tabbatacce ba ne.