Zabura 60
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam* ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri.
Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu;
ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!
Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta;
ka daure karayarta, gama tana rawa.
Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala;
ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.
Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta
don a buɗe gāba da baka.
Sela
 
Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama,
domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki,
“Da nasara zan rarraba Shekem
in kuma auna Kwarin Sukkot.
Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne;
Efraim shi ne hular kwanona,
Yahuda kuma sandar mulkina.
Mowab shi ne kwanon wankina,
a kan Edom zan jefa takalmina;
a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”
 
Wa zai kawo ni birnin katanga?
Wa zai bishe ni zuwa Edom?
10 Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu
ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
11 Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba,
gama taimakon mutum banza ne.
12 Tare da Allah za mu yi nasara,
zai kuma tattake abokan gābanmu.
* Zabura 60: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Zabura 60: Kan Magana. Wato, Arameyawan Arewa maso Yamma na Mesofotamiya. Zabura 60: Kan magana, wato, Arameyawan Tsakiyar Suriya.