Zabura 61
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.
Ka ji kukata, ya Allah;
ka saurari addu’ata.
 
Daga iyakar duniya na yi kira gare ka,
na yi kira yayinda zuciyata ta karai;
ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.
Gama kai ne mafakata,
hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.
 
Ina marmari in zauna a tentinka har abada
in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka.
Sela
Gama ka ji alkawarina, ya Allah;
ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.
 
Ka ƙara kwanakin ran sarki,
shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.
Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada;
ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.
 
Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka
in kuma cika alkawarina kowace rana.