Zabura 63
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda.
Ya Allah, kai ne Allahna,
da nacewa na neme ka;
raina yana ƙishinka,
jikina yana marmarinka,
cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye
inda babu ruwa.
 
Na gan ka a wuri mai tsarki
na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,
leɓunana za su ɗaukaka ka.
Zan yabe ka muddin raina,
kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau;
da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
 
A gadona na tuna da kai;
ina tunaninka dukan dare.
Domin kai ne mai taimakona,
ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
Raina ya manne maka;
hannunka na dama yana riƙe da ni.
 
Su da suke neman raina za su hallaka;
za su gangara zuwa zurfafan duniya.
10 Za a bayar da su ga takobi
su kuma zama abincin karnukan jeji.
 
11 Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah;
dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi,
amma za a rufe bakunan maƙaryata.