Zabura 62
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda.
Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai;
cetona na zuwa daga gare shi.
Shi kaɗai ne dutsena da cetona;
shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
 
Har yaushe za ku tasar wa mutum guda?
Dukanku ne za ku kā da shi
wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga?
Sun kintsa sosai su tumɓuke shi
daga matsayinsa mai martaba;
suna jin daɗi yin ƙarairayi.
Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu,
amma a zuciyarsu la’antawa suke yi.
Sela
 
Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;
dogarata kan zo daga gare shi ne.
Shi ne kaɗai dutsena da cetona;
shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,*
shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;
ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,
gama Allah ne mafakarmu.
Sela
 
Talakawa dai kamar shaƙar iska suke,
Attajirai dai kamar shirim suke;
in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne;
dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.
10 Kada ku dogara a kan ƙwace
ko yin fariya a kayan sata;
ko arzikinku ya ƙaru,
kada ku sa zuciyarku a kansu.
 
11 Abu guda Allah ya ce,
abubuwa biyu na ji,
“Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,
12 kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne.
Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum
bisa ga abin da ya yi.”
* Zabura 62:7 Ko kuwa / Allah Mafi Ɗaukaka shi ne cetona da girmata