Zabura 65
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa.
1 Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona;
a gare ka za mu cika alkawuranmu
2 Ya kai wanda yake jin addu’a
a gare ka dukan mutane za su zo.
3 Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu,
ka gafarta laifofinmu.
4 Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa
ka kawo kusa don su zauna a filayenka!
Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka,
na haikalinka mai tsarki.
5 Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci,
Ya Allah Mai Cetonmu,
begen dukan iyakar duniya
da kuma na tekuna masu nesa,
6 wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka,
bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,
7 wanda ya kwantar da rurin tekuna,
rurin raƙumansu,
da kuma tumbatsar al’ummai.
8 Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka;
inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe
kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.
9 Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa;
kana azurta ta a yalwace.
Rafuffukan Allah sun cika da ruwa
don su ba mutane hatsi,
don haka ne ka ƙaddara.
10 Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta;
ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta.
11 Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka,
amalankenka kuwa sun cika har suna zuba.
12 Makiyayan hamada sun cika har suna zuba;
tuddai sun rufu da murna.
13 Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna
kwari kuma sun cika da hatsi;
suna sowa don farin ciki.