Zabura 66
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura.
Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!
Ku rera ɗaukaka ga sunansa;
ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!
Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke!
Ikonka da girma yake
har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.
Dukan duniya sun rusuna a gabanka
suna rera yabo gare ka,
suna rera yabo ga sunanka.”
Sela
 
Ku zo ku ga abin da Allah ya yi,
ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum!
Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa,
sun wuce cikin ruwaye da ƙafa,
ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.
Yana mulki har abada ta wurin ikonsa,
idanunsa suna duban al’ummai,
kada ’yan tawaye su tayar masa.
Sela
 
Ku yabi Allahnku, ya mutane,
bari a ji ƙarar yabonsa;
ya adana rayukanmu
ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi.
10 Gama kai, ya Allah, ka gwada mu;
ka tace mu kamar azurfa.
11 Ka kawo mu cikin kurkuku
ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.
12 Ka bar mutane suka hau a kawunanmu;
mun bi ta wuta da ruwa,
amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.
 
13 Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa
zan kuwa cika alkawurana gare ka,
14 alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa
sa’ad da nake cikin wahala.
15 Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka
da kuma baye-baye na raguna;
zan miƙa bijimai da awaki.
Sela
 
16 Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah;
bari in faɗa muku abin da ya yi mini.
17 Na yi kuka gare shi da bakina;
yabonsa yana a harshena.
18 Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata,
da Ubangiji ba zai saurara ba;
19 amma tabbatacce Allah ya saurara
ya kuma ji muryata a cikin addu’a.
20 Yabo ga Allah,
wanda bai ƙi addu’ata ba
ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni!