Zabura 68
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura. Waƙa.
Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa;
bari maƙiyansa su gudu a gabansa.
Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka;
kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta,
bari mugaye su hallaka a gaban Allah.
Amma bari adalai su yi murna
su kuma yi farin ciki a gaban Allah;
bari su yi murna da farin ciki.
 
Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,
ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;*
sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,
shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai,
ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi;
amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.
 
Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah,
sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi,
Sela
duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama,
a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai,
a gaban Allah, Allah na Isra’ila.
Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah;
ka rayar da gādonka da ya gāji.
10 Mutanenka suka zauna a cikinsa,
kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta.
 
11 Ubangiji ya yi umarni,
mutane masu yawa ne suka yi shelarsa,
12 “Sarakuna da mayaƙa suka gudu a gaggauce;
cikin sansani mutane sun raba ganima.
13 Har yayinda kuke barci a cikin garken tumaki,
an dalaye fikafikan kurciya da azurfa,
fikafikanta da zinariya mai ƙyalli.”
14 Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa,
sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon.
 
15 Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne;
duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne.
16 Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa,
a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki,
inda Ubangiji kansa zai zauna har abada?
17 Karusan Allah ninkin dubbai goma ne
da kuma dubu dubbai;
Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa.
18 Sa’ad da ka hau bisa,
ka bi da kamammu cikin tawagarka;
ka karɓi kyautai daga mutane,
har ma daga ’yan tawaye,
don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can.
 
19 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu,
wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu.
Sela
20 Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto;
daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa.
21 Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa,
rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa.
22 Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan;
zan kawo su daga zurfafan teku,
23 don ku wanke ƙafafunku a cikin jinin maƙiyanku,
yayinda harsunan karnukanku su sami rabonsu.”
 
24 Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah,
jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki.
25 A gaba akwai mawaƙa, a bayansu akwai makaɗa;
tare da su akwai ’yan mata suna bugan ganguna.
26 Ku yabi Allah cikin taro mai girma;
yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila.
27 Ga ƙaramar kabilar Benyamin, suna jagorance su,
ga babbar ƙungiya shugabannin Yahuda,
ga kuma shugabannin Zebulun da na Naftali.
 
28 Ka bayyana ikonka, ya Allah;
ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā.
29 Saboda haikalinka a Urushalima
sarakuna za su kawo maka kyautai.
30 Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro,
garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai.
Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa.
Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.
31 Jakadu za su zo daga Masar;
Kush za tă miƙa kanta ga Allah.
 
32 Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya,
ku rera yabo ga Ubangiji,
Sela
33 gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama,
wanda yake tsawa da babbar murya.
34 Ku yi shelar ikon Allah,
wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila,
wanda ikonsa yake a cikin sarari.
35 Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki;
Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa.
 
Yabo ya tabbata ga Allah!
* Zabura 68:4 Ko kuwa / ku shirya hanya wa shi da yake hawan ta hamada