Zabura 67
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa.
Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu
yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu,
Sela
don a san hanyoyinka a duniya,
cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.
 
Bari mutane su yabe ka, ya Allah;
bari dukan mutane su yabe ka.
Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki,
gama kana mulkin mutanenka da adalci
kana kuma bi da al’umman duniya.
Sela
Bari mutane su yabe ka, ya Allah;
bari dukan mutane su yabe.
 
Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta
Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.
Allah yă sa mana albarka,
dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.