Zabura 74
Maskil* na Asaf.
Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah?
Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka?
Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa,
kabilar gādonka, wadda ka fansa,
Dutsen Sihiyona, inda ka zauna.
Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai,
dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki.
 
Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu;
suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu.
Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura
don yanka itatuwa a kurmi.
Sun ragargaje dukan sassaƙar katako
da gatura da kuma gudumarsu.
Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus;
suka ƙazantar da mazaunin Sunanka.
Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!”
Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar.
 
Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba;
ba sauran annabawan da suka ragu,
kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba.
10 Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah?
Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne?
11 Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama?
Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su!
 
12 Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa;
ka kawo ceto a kan duniya.
 
13 Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka;
ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye.
14 Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa
ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada.
15 Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka;
ka busar da koguna masu ruwa.
16 Yini naka ne, dare kuma naka ne;
ka kafa rana da wata.
17 Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya;
ka yi rani da damina.
 
18 Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji,
yadda wawaye suka ɓata sunanka.
19 Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji;
kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba.
20 Ka kula da alkawarinka,
domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar.
21 Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya;
bari matalauta da mabukata su yabe sunanka.
22 Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka;
ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini.
23 Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka,
ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi.
* Zabura 74: Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.