Zabura 75
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Kada A Hallaka.” Zabura ta Asaf. Waƙa ce.
Muna maka godiya, ya Allah,
muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa;
mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.
 
Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci;
ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.
Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza,
ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram.
Sela
Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’
ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.
Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama;
kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”
 
Ba wani daga gabas ko yamma
ko hamada da zai ɗaukaka mutum.
Amma Allah ne mai yin shari’a,
yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.
A hannun Ubangiji akwai kwaf
cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji;
yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa
su sha shi tas.
 
Game da ni dai, zan furta wannan har abada;
zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,
10 wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye,
amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”