Zabura 76
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce.
A cikin Yahuda an san Allah;
sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
Tentinsa yana a Salem
mazauninsa yana a Sihiyona.
A can ya kakkarya kibiyoyin wuta,
garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi.
Sela
 
Darajarka tana da haske,
fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
Jarumawa sun zube kamar ganima
sun yi barcinsu na ƙarshe;
ba ko jarumi guda
da zai iya ɗaga hannuwansa.
A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub,
doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
 
Kai kaɗai ne za a ji tsoro.
Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
Daga sama ka yi shelar hukunci,
ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a,
don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar.
Sela
10 Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo,
waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
 
11 Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su;
bari dukan ƙasashen maƙwabta
su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
12 Ya kakkarya ƙarfin masu mulki;
sarakunan duniya suna tsoronsa.