Zabura 78
Maskil* na Asaf.
Ya mutanena, ku ji koyarwata;
ku saurari kalmomin bakina.
Zan buɗe bakina da misalai,
zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā,
abin da muka ji muka kuma sani,
abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana.
Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;
za mu faɗa wa tsara mai zuwa
ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,
ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub
ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila,
wadda ya umarce kakanni-kakanninmu
su koya wa ’ya’yansu,
don tsara na biye su san su,
har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba,
su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.
Ta haka za su dogara ga Allah
ba kuwa za su manta da ayyukansa ba
amma za su kiyaye umarnansa.
Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba,
masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa,
waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba,
waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.
 
Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna,
suka juya da baya a ranar yaƙi;
10 ba su kiyaye alkawarin Allah ba
suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa.
11 Suka manta da abin da ya aikata,
abubuwan banmamakin da ya nuna musu.
12 Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu
a ƙasar Masar, a yankin Zowan.
13 Ya raba teku ya kuma bi da su ciki;
ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango.
14 Ya bishe su da girgije da rana
da kuma haske daga wuta dukan dare.
15 Ya tsage duwatsu a cikin hamada
ya kuma ba su ruwaye a yalwace kamar tekuna;
16 ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga
ya sa ruwa ya gudu kamar koguna.
 
17 Amma suka ci gaba da yin masa zunubi,
suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.
18 Da gangan suka gwada Allah
ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi.
19 Suka yi magana a kan Allah,
suna cewa, “Allah zai iya
shimfiɗa tebur a cikin hamada?
20 Sa’ad da ya bugi dutse,
ruwa ya ɓulɓulo,
rafuffuka suka yi gudu a yalwace.
Amma zai iya ba mu abinci?
Zai iya tanada wa mutanensa nama?”
21 Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai;
wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub,
hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,
22 gama ba su gaskata ga Allah ba
ko su dogara ga cetonsa.
23 Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa
ya kuma buɗe ƙofofin sammai;
24 ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci,
ya ba su hatsin sama.
25 Mutane suka ci burodin mala’iku;
ya aika musu dukan abincin da za su iya ci.
26 Ya saki iskar gabas daga sammai
ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa.
27 Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura,
tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku.
28 Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu,
ko’ina kewaye da tentunansu.
29 Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su,
gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi.
30 Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi,
kai tun ma yana a bakunansu,
31 fushin Allah ya ƙuna a kansu;
ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu,
yana yankan matasan Isra’ila.
 
32 Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi;
duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba.
33 Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza
shekarunsu kuma cikin masifa.
34 A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi;
sukan juyo a natse gare shi.
35 Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu,
cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.
36 Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki,
suna masa ƙarya da harsunansu;
37 zukatansu ba sa biyayya gare shi,
ba su da aminci ga alkawarinsa.
38 Duk da haka ya kasance mai jinƙai;
ya gafarta laifofinsu
bai kuwa hallaka su ba.
Sau da sau ya janye fushinsa
bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.
39 Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai,
iska mai wucewa da ba ta dawowa.
 
40 Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada
suka kuma ɓata masa rai a jeji!
41 Sau da sau suka riƙa gwada Allah;
suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila.
42 Ba su tuna da ikonsa,
a ranar da ya fanshe su daga mai danniya,
43 ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar
abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba.
44 Ya mai da kogunansu suka zama jini;
ba su iya sha daga rafuffuka ba.
45 Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su,
da kwaɗin da suka wahalshe su.
46 Ya ba da hatsinsu ga fāra,
amfanin gonakinsu ga ɗango.
47 Ya lalace inabinsu da ƙanƙara
itatuwan al’ul nasu kuma da jaura.
48 Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara,
tumakinsu ga aradun tsawa.
49 Ya saki musu fushinsa mai zafi,
hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa,
ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.
50 Ya shirya hanya wa fushinsa;
bai tsare ransu daga mutuwa ba
amma ya miƙa su ga annoba.
51 Ya bugi kowane ɗan fari na Masar,
mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham.
52 Amma ya fitar da mutanensa kamar garke;
ya bi da su kamar tumaki ta cikin hamada.
53 Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro;
amma teku ya cinye abokan gābansu.
54 Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki,
zuwa ƙasar tudun da hannunsa na dama ya kame.
55 Ya kori al’ummai a gabansu
ya rarraba ƙasashensu gare su a matsayin gādo;
ya zaunar da kabilan Isra’ila a gidajensu.
 
56 Amma suka gwada Allah
suka tayar wa Mafi Ɗaukaka;
ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.
57 Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci,
marar tabbas kamar tanƙwararren baka.
58 Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu;
suka tayar da kishinsa da gumakansu.
59 Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai;
ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.
60 Ya yashe tabanakul na Shilo,
tentin da ya kafa a cikin mutane.
61 Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta,
darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.
62 Ya ba da mutanensa ga takobi;
ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.
63 Wuta ta cinye matasansu maza,
’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure;
64 aka karkashe firistocinsu,
gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.
 
65 Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa,
kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi.
66 Ya kori abokan gābansa;
ya sa suka sha madawwamiyar kunya.
67 Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf,
bai zaɓi kabilar Efraim ba;
68 amma ya zaɓi kabilar Yahuda,
Dutsen Sihiyona, wanda ya ƙaunaci.
69 Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa,
kamar duniyar da ya kafa har abada.
70 Ya zaɓi Dawuda bawansa
ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki;
71 daga kiwon tumaki ya kawo shi
don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub,
na Isra’ila gādonsa.
72 Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya;
da hannuwa masu gwaninta ya bi da su.
* Zabura 78: Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.