Zabura 79
Zabura ta Asaf.
Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka;
sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki,
sun bar Urushalima kufai.
Sun ba da gawawwakin bayinka
kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama,
nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.
Sun zubar da jini kamar ruwa
ko’ina a Urushalima,
kuma babu wani da zai binne matattu.
Mun zama abin reni ga maƙwabta,
abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
 
Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne?
Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta?
Ka zuba fushinka a kan al’umman
da ba su yarda da kai ba,
a kan mulkokin
da ba sa kira bisa sunanka;
gama sun cinye Yaƙub
suka lalatar da ƙasar zamansa.
 
Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu;
bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu,
gama mun fid da zuciya sarai.
Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,
saboda ɗaukakar sunanka;
ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu
saboda sunanka.
10 Don me al’ummai za su ce,
“Ina Allahnsu yake?”
 
A idanunmu, ka sanar wa al’ummai
cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar.
11 Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka;
ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.
12 Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai
zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.
13 Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka,
za mu yabe ka har abada;
daga tsara zuwa tsara
za mu yi ta ba da labarin yabonka.