Zabura 8
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.* Zabura ta Dawuda.
Ya Ubangiji, shugabanmu,
sunanka da girma take a cikin dukan duniya!
 
Ka kafa ɗaukakarka
bisa sammai.
Daga leɓunan yara da jarirai
ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka
da masu ɗaukan fansa su yi shiru.
Sa’ad da na dubi sammai,
aikin yatsotsinka,
wata da taurari
waɗanda ka ajiye a wurarensu,
wane ne mutum da kake tunawa da shi,
ɗan mutum da kake lura da shi?
 
Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah
ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;
ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,
dukan shanu da tumaki,
da kuma namun jeji,
tsuntsayen sararin sama
da kifin teku,
da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
 
Ya Ubangiji, shugabanmu,
sunanka da girma take a cikin dukan duniya!
* Zabura 8: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. Zabura 8:5 Ko kuwa da rayayyun sama