Zabura 7
Wani shiggayiyon* ta Dawuda, wanda Ya Rera wa Ubangiji game da Kush mutumin Benyamin.
Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka;
ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na,
in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki
su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba.
 
Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure
aka kuwa sami laifi a hannuwana,
in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni
ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana,
to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini;
bari yă tattake raina a ƙasa
ya sa in kwana a ƙura.
Sela
 
Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka;
ka tashi gāba da fushin abokan gābana.
Ka farka, Allahna, ka umarta adalci.
Bari taron mutane su taru kewaye da kai.
Ka yi mulki a bisansu daga bisa;
bari Ubangiji mai shari’ar mutane.
Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina,
bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka.
Ya Allah mai adalci,
wanda yake binciken tunani da zukata,
ka kawo ƙarshen rikicin mugaye
ka kuma sa adalai su zauna lafiya.
 
10 Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka,
wanda yake ceton masu tsabtar zuciya.
11 Allah alƙali ne mai adalci,
Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana.
12 In mutum bai tuba ba,
Allah zai wasa takobinsa;
zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa.
13 Ya shirya makamansa masu dafi;
ya shirya kibiyoyinsa masu wuta.
 
14 Wanda yake da cikin mugunta
ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya.
15 Wanda ya haƙa rami
yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa.
16 Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa;
fitinarsa takan sauka a kansa.
 
17 Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa
zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.
* Zabura 7: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce.