Zabura 81
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.* Ta Asaf.
Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu;
ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!
Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga,
ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.
 
Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata,
da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;
wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila,
farilla ta Allah na Yaƙub.
Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf
sa’ad da ya fito daga Masar.
 
Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.
 
Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku;
an ’yantar da hannuwansu daga kwando.
Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku,
na amsa muku daga girgijen tsawa;
na gwada ku a ruwan Meriba.
Sela
 
“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku,
in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!
Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku;
ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.
10 Ni ne Ubangiji Allahnku
wanda ya fitar da ku daga Masar.
Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.
 
11 “Amma mutanena ba su saurare ni ba;
Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.
12 Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare
don su bi dabararsu.
 
13 “A ce mutanena za su saurare ni,
a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,
14 da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu
in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!
15 Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki,
hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.
16 Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau;
da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”
* Zabura 81: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.