Zabura 82
Zabura ta Asaf.
Allah yana shugabanta cikin babban taro;
yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.
 
“Har yaushe za ku kāre marasa adalci
ku kuma goyi bayan mugaye?
Sela
Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu;
ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.
Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata;
ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.
 
“Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba.
Suna yawo cikin duhu;
an girgiza dukan tussan duniya.
 
“Na ce, ‘Ku “alloli” ne;
dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.
Amma za ku mutu kamar mutum kurum;
za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”
 
Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya,
gama dukan al’ummai gādonka ne.