Zabura 84
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce.
1 Ina misalin kyan wurin zamanka,
Ya Ubangiji Maɗaukaki!
2 Raina yana marmari, har yana suma,
don filayen gidan Ubangiji;
zuciyata da namana na tā da murya
domin Allah mai rai.
3 Har tsada ma ta sami gida,
tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa,
inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta,
wuri kusa da bagadenka,
Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.
4 Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka;
kullum suna ta yabonka.
Sela
5 Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka,
waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.
6 Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka,
sukan mai da shi wurin maɓulɓulai;
ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.
7 Suna ta ƙara ƙarfi,
har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.
8 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki;
ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub.
Sela
9 Ka dubi garkuwarmu, ya Allah;
ka duba da alheri a kan shafaffenka.
10 Rana guda a filayen gidan sun fi
dubu a wani wuri dabam;
zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna
da in zauna a tentunan mugaye.
11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;
Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;
ba ya hana kowane abu mai kyau
wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
12 Ya Ubangiji Maɗaukaki,
mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.